Main menu

Pages

Yanda zaka gyara youtube dinka idan yana maka slow ko baka matsala wajen dora bidiyo

Yanda zaka gyara YouTube dinka idan baya aiki ko idan yana baka matsala wajen uploadingAssalamu Alaikum


Ka gyara matsalolin YouTube channel dinka ya dawo aiki ba dare ba rana.


A yau YouTube yana fuskantar matsaloli da yawa daga sassan kasashen duniya. Rahotanni daga manhajar Twitter na cewa bidiyoyi da dama basa hawa kan YouTube app daga mafi yawancin mutanen da suke oflodin bidiyo nasu. Amma kuma shafin yanar gizo na YouTube kuma yana aiki lafiya-lafiya.


Haka zalika YouTube team suma sun amsa korafin da yake yawo akan Twitter cewar suna sane da matsalar kuma suna kan aikin gyarawa. ’Yan kwanakin nan YouTube yana dan bada matsala wajen nauyi da oflodin.


Idan kana fuskantar matsaloli da YouTube , ranka ya huta kaji kamar ba kai kadai bane. Ka jarraba wasu daga cikin wadannan dabarun na kasa domin mayar da YouTube channel dinka yake aiki.


YouTube shine mafi girman wurin baza hajar bidiyoyi na online a fadin duniya, tare da sama da mutum biliyan biyu da miliyan dari uku masu amfani dashi ko wane wata. Idan YouTube ya kasance baya aiki, hakan yana fassara matsala ta samu a wurin mutane da dama, so meya kamata kayi idan ka samu kanka acikin irin wannan halin? Anan ga wasu abubuwa da zaka gwada akan wayarka ta Android da kuma na’urar kwamfuta wato Windows devices.


1. Fara dubawa idan YouTube app din yayi kasa


Wannan ba bakon al’amari bane, wasu lokutan YouTube yakan yi kasa. Wannan shine abu na farko da zaka duba. Babu wata hanya kai-tsaye da zaka gane idan server ta YouTube bata aiki, amma ga wasu ’yan matakai da zamu baku.


Zaka iya samun bayanai idan ka tafi kai-tsaye zuwa asusun YouTube na Twitter. Dukkan wasu korafe korafe daya shafi YouTube zaka same shi anan.


Sannan muna son fada uku wani shafi na Down Detector, shafi ne da mutane suke bayyana matsalolinsu da suka shafi YouTube idan baya aiki. Shafin yawanci zaka samu amsa nan take, sannan yana dauke da live map ta yadda zaka gane duk wata hanya da/ko rashin network ne ya jawo hakan.


Idan YouTube ya kasance yana down, babu wani abu da zaka iya face ka jira na dan wani lokaci.


2. Rufewa da sake budewa aflikeshon din ko website


Cikin sauki rufewa da sake budewa YouTube app yakan magance wasu kananan matsaloli ko makalewa. Idan kana amfani da kwamfuta, zaka iya rufe ko dai tab ko kuma browser sannan ka sake gwada shiga YouTube din.


3. Yawan kula da ofdet


Idan ya kasance YouTube app din tsohon versions ne bashine kadai matsalar ba, amma wasu lokutan yakan haifar da rashin jituwa. Wannan matsalar musamman a yawan yin ofdet, ko kuma ofgired daya ke dauke da sauye-sauyen server. Ka tabbatar dai kana amfani da lates bashon na YouTube app din.


Zai iya taimakawa kuma idan kaga komai daban sun zama updated. Saika duba idan akwai updates daya ke abailabil na browser naka (idan kana amfani da ita). Idan kuma kana amfani da wayar Android, ka duba idan akwai wani available updates daya dace da wayarka.


Yanda zaka duba updates a wayar Android:


1. Ka bude Settings app


2. Ka tafi zuwa System


3. Saika taba System update


4. Saika zabi Check for update


5. Sai kabi sharudan da aka baka idan akwai available update din.


4. Sake kunna wayarka/kwamfuta 


A koda yaushe troubleshooting shine matakin farko da ake gano matsalar na’ura! Shine ka danne makunnar wayarka, bayan ta nuna maka zabi saika danna Power off.


5. Ka duba dai-dai tuwar intanet dinka 


Akwai yiyuwar  kwanekshon na intanet ne! Zaka iya jarraba sauran apps da suke amfani da intanet kwanekshon dan su bude kaga idan sunayi. Ka kuma bude browser da Google da komai ma. Idan babu wani acikinsu daya bude, to watakila kana offline.


Ka sake dubawa idan Wi-Fi dinka a kunne yake, ko watakila bisa kuskure ka saka wayarka a jirgi (airplane mode). Wadancan apps da suke amfani da Wi-Fi ko LAN zasu gano maka hanyar da idan ma wayarka tana hade da intanet.


Idan kuma kana amfani da datar waya, zaka iya ganin idan datar wayarka a kunne take:


1. Ka bude Settings app


2. Ka tafi cikin Network & internet


3. Saika zabi SIMs


4. Saika kunna Mobile data on


5. Idan kana wajen kasarka ko network coverage, saika kunna Roaming (amma zasu cajeka kudi).


6. Ka goge tarkacen cache na YouTube aflikeshon din da data


A cikin jerin yadda zaka magance irin wannan matsalar, mai biyowa baya shine sharewa YouTube cache da data. Shi wancan shine gogewa bayanai na dan wani lokaci wato temforari, amma wannan shine kawar da dukkan app data din, wadda ya hadar da saituna da yawa. Wannan zai taimaka saboda wasu lokutan data da settings suna lalacewa, ko makalewa. Amma gogewa komai zai baka damar farawa lafiya lau.


Yanda zaka share cache na YouTube app akan Android:


1. Ka bude Settings app


2. Ka tafi cikin Apps


3. Ka nemi sannan ka taba YouTube app a karkashin See all apps


4. Saika taba kan Storage & cache


5. Saika daki Clear Cache


6. Zaka kuma iya zabar Clear storage domin restart lafiya.


Yanda zaka share cache akan Chrome na Windows:


1. Akan windows na kwamfutarka, ka bude Chrome


2. Saika danna alamun digo guda uku a can sama kwanar dama


3. Ka tafi cikin Settings


4. Saika zabi Security and Privacy a madannin dake hagu


5. Saika dauki Clear browsing data


6. Saika duba akwatinan saika zabi abin da kake son gogewa. Ina son share komai idan akwai matsala babba


7. Saika zabi All time a cikin Time range.


8. Saika daki Clear data

.

7. Kayi sayinkuronayiz na lokaci da kwanan wata


Zai iya zama tsoho, amma lokaci da kwanan wata zai iya zama dalili ga YouTube yaki aiki. Domin kuwa server ta Google tana shan wahalar syncing idan baka saita su dai dai ba.


Sync kwanan wata da lokaci:


1. Ka bude Settings app


2. Ka taba System


3. Ka tafi cikin Date & time


4. Saika kunna shi zuwa Set time automatically


5. Saika kunna Set time zone automatically


6. Saika kunna Use location to set time


Yanda zaka saita lokaci da kwanan wata akan Windows:


1. Ka bude Settings app


2. Ka tafi cikin Time & Language


3. Saika zabi Date & time a gefen hannun hagu


4. Saika kunna shi zuwa Set time automatically


5. Saika sake kunna Set time zone automatically


Shin netwok yana rufe YouTube?


A wasu lokutan akwai netwok restirikshon akan YouTube dama sauran services. Wannan abune mai sauki kaga lokacin da kake amfani da yanar gizo daga makaranta, library ko wasu wurare inda administrator basa sonka da kallon bidiyoyi barkatai. Mafita daya akan wannan matsalar itace a tambayi administrator su bada damar shiga YouTube. Za kuma ka iya kunna datar wayarka ko kayi amfani da available network.


8. Ofdet na GPU diraiba


Idan kana amfani da YouTube akan kwamfuta kuma kake da matsala tare da shi akan baya aiki, akwai yiyuwar matsala tattare da GPU (graphics processing unit). Ka gwada updating driver din kaga idan zai hakan zai taimaka. Kasa a ranka cewa wannan yana magance matsalar masu amfani da kwamfuta ne kadai. Ka wuce wannan bangaren idan baka amfani da kwamfuta.


Yanda zakayi updating na GPU driver akan Windows:


1. Akan windows search bar, ka rubuta Device Manager, saika bude app din


2. Ka buda bangaren Display adapter


3. Saika danna right-click akan GPU dinka


4. Saika zabi Update driver


5. Ka danna kan Search automatically for driver


6. Ka bar kwafutar tayi aikin ta sannan ka bi sharudan da aka baka.


9. Ka kashe hadwaya aselareshon


Ka taba samun baki ko koren screen alhalin kana kokarin kunna YouTube video? Matsalar bata da dadi sam, musamman lokacin da baka san menene ya janyo hakan ba kuma baka san yadda zaka magance matsalar ba. Yawanci hakan yakan zone sakamakon hardware acceleration. Ka gwada kashe ta.


Yanda zaka kashe hadwaya aselareshon akan Chrome ta Windows:


1. Ka bude Chrome akan kwamfutarka


2. Ka danna digon nan guda uku a sama kwanar dama


3. Saika zabi Settings


4. Saika fadada Advanced section


5. Ka tafi cikin System


6. Saika kashe hardware acceleration when available option.


                                                                        


Shin YouTube yaci gaba da bada matsala bayan gwada wadannan? Watakila lokaci yayi da zaka tura matsalar ka zuwa YouTube team domin karin bayani.Allah ya taimaka.


Comments